YouTube kafar sadarwa ce da kuma dandalin watsa bidiyoyi tayanar gizo taAmurka wanda kamfaninGoogle ta mallake ta.Steve Chen,Chad Hurley, da kumaJawed Karim ne suka ƙirƙiri Youtuba a ranar 14 ga Fabrairu, 2005, tsofaffin ma'aikatan KamfaninPayPal. Hedikwata na San Bruno,California, Amurka, kuma a halin yanzu itace kafar yanar gizo na biyu da aka fi ziyarta, bayanGoogle Search. A cikin watan Junairun 2024, YouTube tana da masu amfani da ita fiye da biliyan 2.5 a kowane wata, waɗanda ke kallon sama da sa'o'i biliyan ɗaya na bidiyoyi a kowace rana.[1] Tun daga watan Mayun 2019, ana loda bidiyoyi aƙalla sama da sa'o'i 500 a duk bayan minti daya,[2][3] sannan kuma ya zuwa shekara ta 2023, akwai aƙalla bidiyoyi biliyan 14 gaba daya.[4]
Google ta siya Youtube a ranar 9 ga watan Oktoban 2006, akan kudi $1.65 (daidai da dala biliyan $2.31 a cikin shekara ta 2023),[5] Google ta fadada salon kasuwancin Youtube ta hanyar samar da kudin shiga don tallace-tallace, da samar da biyan kudi ga bidioyi kamar fina-finai da kuma masu kirkirar bidiyoyi na musamman a Youtube ko don saboda ita. Har wayau, tana samar da tsarinYouTube Premium, wani tsari na biya don kallo a Youtube ba tare da tallace-tallace ba. Youtube ta shigo da shirinGoogle's AdSense don samar da kudin shiga ga ita Youtube da kuma masu kirkira da aka yarje mawa. A cikin shekara ta 2023, kudin shiga na Youtube ya kai adadin dala biliyan $31.7, an samu karin kashi 2% daga $31.1 kamar yadda aka sanar a shekara ta 2022.[6] Daga ƙarshen watannin shekara ta 2023 zuwa tsakiyar watannin shekara ta 2024, adadin kudin shiga na Youtube daga tallace-tallace da kuma biyan kudi sun haura dala biliyan 50.[7]
Tun bayan da Google ta siye ta, Youtube ta fadada fiye da shafin yanar gizo zuwa app na waya, tashar telebijin, da kuma damar ta na hadaka da wasu kafofin. Nau'in bidiyoyi a Youtube sun hada da bidiyoyin waka, hotunan bidiyo, gajerun bidiyoyi, labarai, fina-finai, wakoki, labarun gaskiya, tallar fina-finai, tashar wasanni, kallo na kai tsaye, da dai sauran su. Mafi yawanci mutane ne ke kirkirar bidiyoyi a cikinta, wanda ya hada da hadaka a tsakanin 'Yan-Youtube da kuma masu daukan nauyinsu. Manyan kafofin midiya, labarai, da masana'antun nishadantarwa sun kirkira kuma sun karawa kawunansu shahara ta hanyar Youtube don riskar mutane da dama.
Youtube ta yi tasiri sosai a fannin zamantakewa, tayi tasiri akan fitattun al'adu, yayi na yanar gizo, kuma ta samar da shahararrun manyan masu kudi. Duk da nasarorinta, an soki kafar da assasa yaduwar ƙarerayi, da tauye haƙƙoƙin mallaka, cigaba da ƙetare sirrikan masu amfani da ita, tsauraran dokoki, da kuma sanya rayuwar yara acikin hatsari, da kuma rashin tsayayyen aiwatar da ƙa'idojin kafar.
Dangane da wani labari da ake yawan fada a midiya, Hurley da Chen ne suka kirkiri dabarar Youtube a farkon shekara ta 2005, bayan sun sha wahalar watsa bidiyo da aka dauka a wajen fati na dina a gidan Chen aSan Francisco. Karim bai halarci fatin ba kuma ya musunta faruwar hakan, amma kuma Chen ya bayyana cewa an kirkiri dabarar Youtube ne a wajen wani fati na dina ya kasance watakila dalilin da ya kara karfafawa 'yan kasuwa ra'ayin kirkirar labarin da za'a iya yarda da shi.[10]
Karim yace, dabarar Youtube ya zo ne daga Rikicin wasan hutun rabin sa'a na Super Bowl XXXVIII a yayin daJustin Timberlake ya ɗan bayyana nononJanet Jackson a yayin hutun rabin sa'a. Karim ya sha wahalar gano bidiyon da kuma bidiyon ambaliyar ruwa a tekun Indiya na 2004 a yanar gizo, wanda ya janyo dabarar kirkiran shafin watsa bidiyoyi ta yanar gizo.[11][12] Hurley da Chen sun ce asalin dabarar Youtube ya zo ne daga wani nau'in bidiyo na shafin sada alaka ta yanar gizo kuma ya tasirantu daga wani shafin yanar gizo mai sunaHot or Not.[10][13] Suna turawa kyawawan mata sako aCraigslist suna ce musu su sanya bidiyoyinsu a shafin don samun kyautan dala $100.[14] Wahala don samun isassun bidiyoyin alaka ya janyo sauya dabara, inda wanda suka kirkiri shafin suka amince a rika daura kowanne irin bidiyo.[15]
↑Helft, Miguel; Richtel, Matt (October 10, 2006). "Venture Firm Shares a YouTube Jackpot".The New York Times. ProQuest 433418867. Archivedfrom the original on March 11, 2021. Retrieved March 26, 2017.