Movatterモバイル変換


[0]ホーム

URL:


Jump to content
WikipediaInsakulofidiya ta kyauta
Binciko

Yaƙin Duniya na II

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentYaƙin Duniya na II
WWII,WW2,SWW daSGM

Iriworld war(mul)Fassara
historical period(en)Fassara
Kwanan watan1 Satumba 1939 –  2 Satumba 1945
Zangon lokacinewest history(en)Fassara dalate modern period(en)Fassara
WuriRasha
Turai
Afirka
Pacific Ocean
Bahar Rum
Asiya
Tekun Atalanta
Gabas ta tsakiya
Southeast Asia(en)Fassara
Scandinavia(en)Fassara
Yakin Pacific
Battle of the Atlantic(en)Fassara
Tekun Indiya
South Asia(en)Fassara
Arewacin Asiya
Sin
Japan
Kudancin Afirka
Gabashin Afirka
Afirka ta Tsakiya
Asturaliya
Amirka ta Arewa
Amurka ta Kudu
Participant(en)Fassara
SanadiSecret Additional Protocol to the Molotov–Ribbentrop Pact(en)Fassara
Yana haddasaBritish pet massacre(en)Fassara
The Holocaust
atomic bombings of Hiroshima and Nagasaki(en)Fassara
Bombing of Dresden(en)Fassara
Allies of World War II(en)Fassara
Nazi Germany(en)Fassara
Dai-Nippon Teikoku(mul)Fassara
Allied-occupied Germany(en)Fassara
Austriya
League of Nations(en)Fassara
Majalisar Ɗinkin Duniya
Tarayyar Amurka
Kungiyar Sobiyet
Cold War
Japan
Korean Peninsula(en)Fassara
Soviet invasion of Poland(en)Fassara
Nazi persecution of the Catholic Church in Poland(en)Fassara
Adadin waɗanda suka rasu73,000,000
Hanyar isar da saƙo
Has part(s)(en)Fassara
Yakin Pacific
Big Week(en)Fassara
Bloody Sunday(en)Fassara
Attack on Pearl Harbor(en)Fassara
Operation Barbarossa(en)Fassara
Battle of Madagascar(en)Fassara
Military occupation of the Slovak Republic(en)Fassara
Battle of France(en)Fassara
German occupation of Norway(en)Fassara
Third Battle of Kharkov(en)Fassara
Axis occupation of Greece(en)Fassara
Battle of the Scheldt(en)Fassara
Middle East Theater of World War II(en)Fassara
Battle of Britain(en)Fassara
Battle of the Atlantic(en)Fassara
Eastern Front(en)Fassara
Battle of Aachen(en)Fassara
Normandy landings(en)Fassara
Operation Flashpoint(en)Fassara
Battle of the Bulge(en)Fassara
Mediterranean and Middle East Theater of World War II(en)Fassara
country in World War II(en)Fassara
#(mul)Fassara#world_war_ii
Bayan harin bom na Vallø a Norway, Afrilu 1945 (WWII)

Yaƙin Duniya na (2) da turanciWorld War II akan kintse rubutun kamar hakaWWII koWW2, har yau ana ƙiran shi da turanciSecond World War. Yaƙin duniya dai wani yaƙine daduniya baki ɗaya suka afka a ciki wanda ya kwashi tsawon shekaru shida (6) ana gwabzawa, tun daga shekara ta alif (1939) har zuwa shekara ta alif (1945) Mafiya yawan ƙasashen duniya tare da ƙasashe masu ƙarfi su ne suka ja daga a tsakanin su, inda suke yaƙan juna: Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda aƙalla mutane sama da miliyan ɗari ne (100,000,000) suka tsunduma a ciki daga ƙasashe sama da talatin (30). Mafiya yawan ƙasashen da suka shiga cikin yaƙin sun saka dukkan tattalin arziƙin su, da kumaMasana'antunsu da ilimin su na kimiyya da fasaha don ganin sun yi galaba a yaƙin. Yaƙin duniya na II shi ne yaki mafi muni a duniya wanda Dan Adam bai taɓa gani ba, inda aka samu rasa rayukan mutane daga miliyan (50) zuwa miliyan (85)yawan cinsu fararen kaya ne daga ƘasarSoviet Union watoRasha a yanzu da kuma ƘasarSin. An kuma sami kashe-kashe, kisan kiyashi akanYahudawa, tsarin jefa bama-bamai, mutuwa sanadiyyar yunwa da cututtuka, da kuma amfani da makaman kare-dangi a yaƙinAtomic Weapeons.

Ansoma yaƙin ne daga rana ga watan Satumba, shekara ta alif (1939) zuwa ranar (2) ga watan Satumba, shekara ta alif (1945) tsawon shekaru (6 da kwana daya 1)

Ƙasashen ƙawanceAllied Countries sunyi nasara, an kifar da Gwamnatin Nazi dakeJamus, An samu faɗuwar Daulolin yankinJapan danaItaliya, Anfara amfani da Makaman kare dangi watoAtomic weapons, Inganta ayyuka da jiragen sama, rusa kungiyar League of Nations, ƙirƙirarMajalisar Dinkin Duniya watoUnited Nations, Fara ƙiyayya tsakanin ƘasarAmurka daRasha, fara yaƙin mummuƙe watoCold war. Jagororin ƙungiyar ƙawance na Kasa da kasa,

Kwamandodi da Shuwagabanni

[gyara sashe |gyara masomin]
  1. Soviet UnionJoseph Stalin
  2. United StatesFranklin D. Roosevelt
  3. United KingdomWinston Churchill
  4. Jamhoriyar Sin (1912–1949)Chiang Kai-shek

Waɗanda ake faɗa dasu:

  1. Nazi GermanyAdolf Hitler
  2. Masarautar JapanHirohito
  3. Masarautar ItalyBenito Mussolini

Abubuwan da akayi asaransuAn kashe Sojoji:Sama da miliyan (16,000,000) An kashe farin kaya:Sama da million (45,000,000)Adadin rayukan da aka rasa:Sama da miliyan (61,000,000)(1937–1945)

ƙasar Japan da ke son ta mamaye nahiyar Asiya da yankin Pacific, ta fara yaƙi da Ƙasar Sin tun daga shekara ta alib (1937) duk da cewar babu ɓangaren da yafito a fili ya ayyanar da yaki akan wanin sa. Ana dai ganin yakin ya soma ne a (1) ga watan Satumbar, shekara ta alib (1939) bayan mamaye ƙasarPoland da ƙasar Jamus tayi, da kuma ƙaddamar da yaƙi da ƘasarFaransa daIngila sukayi akan ƙasar Jamus a ƙarshen shekarar (1939)nhar zuwa farkon shekara ta (1941) sai dai irin gumurzu da shirin da Jamus din tayi ne, hakan yasa ta samu nasarar mallakar kusan duka nahiyarTurai, kuma sai suka kulla ƙawance da ƙasar Italiya da Japan (Axis powers) a ƙarƙashin yarjejeniyarMolotov–Ribbentrop Pact of August (1939),Jamus da ƙasar Soviet sun rarraba tare da mallakar yankunan Turai na ƙasashe kamar irin su Poland, Finland, Romania da jihohin dake Baltic. Bayan fara yaƙi akan ƙasashen dake yankinAfirka ta arewa da Afirka ta gabas, da kuma faɗuwar ƙasar Faransa a tsakiyar shekarar (1940) Yaƙin ya koma mafi yawanchi tsakanin ƙasashenJamus,Italiya da kumaDaular Romania akanDaular Biritaniya. Sai kuma fara Yaƙi a Balkans,Da kuma Fafatawar sararin samaniya aIngila watoAerial Battle of Britain da kuma harin sama tare dayin ruwan bomabomai da ƙasarJamus din tayi waBirtaniya watoBlitzkrieg, sai kuma fafatawar MallakarTekun Atlantik da ya biyo baya, Ana Chikin wannan Bala'in ne sai kuma Ƙasashen haɗakar (Axis Powers) a turai suka ƙaddamar da hari akan kasar Soviet Union (Rasha) watoOperation Barbarossa a ranar (22) ga watan june, shekara ta alib (1941) hakan yasa suka bude wani sabon shafin yaƙin mafi muni a tarihi, A kuma watan December, shekara ta alib (1941) Japan ta ƙaddamar da wani hari a kasar da wasu yankunan turawa dake yankin tekunPacific. Hakane yasa kasar taAmurka ta shiga Yaƙin a gefenAllied Countries kuma ta Ayyana yaƙi akan ƙasar Japan, hakan yasa ta samu goyon bayan kasarBiritaniya, amma sai ƙasashen dake ƙawance da Japan na turawa suma suka mara wa Japan din baya, hakane yasa Japan ta ƙwace yawancin yankunan turawa dake yankin tekun Pacific, wanda yawancin kasashenAsiya suke ganinsa a matsayin wani shiri ne daga ƙasashen yamma na yin mamaye a yankunan su, amma kuma bayan ƴanWatanni da suka gane wa idanuwan su irin zalunchin daAxis Powers keyi yasa dagabisani ra'ayin mutanen ƙasashen ya juya akan su.Yaki ya tsaya a shekara ta (1945) bayan Japan ta miƙa wuya, kuma Jamus da Italiya suma anyi galaba akanmsu a arewacin Afirka da gabashin ta, da kuma gagarumar nasarar daRed Army suka yi akan jamus da Italiya a garin Stalingrad dake Soviet Union a shekara alib (1943) da kuma mamaye Sicily da Italiya, da nasarar ƙasashen kawance (Allied Powers) a yankin Pacific, a shekara ta alib (1944) kasashen ƙawance sun ƙwace yankin Faransa daga hannun Jamus watoD-day Invasion kuma itama ƙasar Soviet Union ta dawo da duka yankunan ta daga hannun Jamus da ƙawayenta. Sa'annan kuma a shekara ta alib (1944) zuwa shekara ta alib (1945)ƙasar Japan ta sha kashi sosai a yankin Asiya, musamman a fafatawar da suka yi da Amurka aTekun Pacific watoBattle Of Midway,da kuma tsakiyar ƙasar Sin da kasarBurma, hakan ya sanya su rasa dukkanin yankunan da suka mamaye.

Yaƙi a nahiyar turai ya ƙare ne sanadiyar mamaye Jamus da ƙasashen kawance (Allied Countries) da ƙasar Soviet suka yi wanda yakai ga kama garin Berlin da mutuwarAdolf Hitler da miƙa wuyan da Jamus tayi a 8 ga watan May, shekara ta alib (1945) BayanPotsdam Declaration daga ƙungiyar ƙawance a( 26) ga watan July, shekara ta alib (1945)

yakin duniya na biyu

ƙin da ƙasar Japan tayi na miƙa wuya, yasa ƙasar Amurka ta jefa mata Makamin ƙare dangi watoatomic bomb a garuruwanHiroshima daNagasaki a (6) da (9) ga watan Augusta. Da kuma mamaye tsibirinarchipelago imminent, da ganin irin asarar rayukan da ake yi, da kuma mamayen yankuna da kasar Soviets ta ke chi gaba dayi a garuruwan Manchuria da tsibirin Kuril dake arewacin ƙasar ta Japan, hakan yasa Sarkin ƙasar japan watoHirohito a (2) ga watan satumba, shekara ta alib (1945) ya miƙa wuya, wannan ya bada damar yin nasarar sojojin ƙawance a nahiyar Asiya, sai kuma aka fara tuhumar kasar Jamus da japan akan laifukan yaƙi a kotunanInternational Military Tribunal (IMT) da kumaThe International Military Tribunal For The Far East ko kuma (IMTFE).

Manazarta

[gyara sashe |gyara masomin]
Wannan Muƙalarguntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iyagyara ta.
Daga "https://ha.wikipedia.org/w/index.php?title=Yaƙin_Duniya_na_II&oldid=743068"
Rukunoni:

[8]ページ先頭

©2009-2026 Movatter.jp