the free encyclopedia that anyone can edit,الموسوعة الحرة التي يستطيع الجميع تحريرها,vapaa tietosanakirja,de vrije encyclopedie,свободная энциклопедия, которую может редактировать каждый,Die freie Enzyklopädie,人人可编辑的自由百科全书,人人可編輯的自由百科全書,একটি উন্মুক্ত বিশ্বকোষ, যা সবাই সম্পাদনা করতে পারে,ウィキペディアは誰でも編集できるフリー百科事典です,L'enciclopèdia de contingut lliure que tothom pot millorar,Төрлө телдә яҙылған, сикләүһеҙ ҡулланыуҙа булған ирекле интернет энциклопедия. Һәр кем уны төҙөүҙә ҡатнаша ала,آزاد دائرۃ المعارف جس میں کوئی بھی ترمیم کر سکتا ہے,la enciclopedia de contenido libre que todos pueden editar,a szabad enciklopédia,Ազատ հանրագիտարան, որը կարող է խմբագրել յուրաքանչյուր ոք:,האנציקלופדיה החופשית שכולם יכולים לערוך,Wolna encyklopedia, którą każdy może redagować,海納百川,有容乃大,la libera enciklopedio redaktebla de ĉiuj dasebuah ensiklopedia bebas yang bisa disunting oleh siapa saja
WikipidiyaInsakulofidiya ce ta kyauta da ke tattare da harsuna daban-daban a faɗinduniya, wanda al'ummomi masu bada gudummawa ke rubuta mukalai ta hanyar haɗin gwiwa a fili (ba tare da ɓoye-ɓoye ba). A turance a na kiran editocinta da sunaWikipedians. Wikipidiya ta kasance farfajiyar nazari mafi girma a tarihin ilimin duniya.[1] Ta kasance ɗaya daga cikin fitattun shafukanyanar gizo guda goma a duniya kamar yadda Similarweb ta zayyano; izuwa shekara ta 2022 kuwa, Wikipidiya itace ta 7 a cikin jerin fitattun shafuka na yanar gizo a duniya.[2][3][4] gidauniyarWikimedia Foundation ce ke daukan nauyin shafin wikipidiya. ita kuwaWikimedia Foundation wata kungiya ce wanda ba'a samar da riba (wato non-profit organization a Turance) na kasar Amurka, kuma suna samun kudadensu ne ta hanyar taimako/gudummawa (donation) daga wasu kungiyoyi kojama'a.[5]
tambarin shafin WikipediaJimmy Wales babban shugaban Wikipedia kuma wanda yasamar da ManhajarLarry Sanger mutum na biyu da suka ƙirƙiri Manhajar Wikipedia
Wikipedia shafi ne nayanar gizo wanda masu bada gudummawa ke rubuta muƙalai kuma su ke gudanar da ita, ta hanyar shigar da ilimi ko gyare-gyare da sauransu. A Turance ana kuma kiran duk wani mai gyare-gyare ko shigar dailimi a shafukan Wikipedia da suna "Wikipedian". Wikipidiya tana tattare da harsunanduniya da dama, a shafinta kowa na iya ƙirƙira ko gyara muƙala a kyauta domin taimakawa wajen samar da ilimi kyauta, wannan ne yasa wikipidiya tayi zarra a duk duniya wurin samar da ilimi daga asalin inda ilimin ya fito.
Kowa da kowa na da damar bada gudummawa wajen yaɗa ilimi ta hanyar ƙirƙiran sabuwar muƙala ko gyara ƙirƙirarrun muƙalai da ke buƙatan a ingantasu ta hanyar gyara wasu 'yan kura-kurai ko ƙarin bayani. Harwayau babu wani shafi a duniya baki ɗaya da ya tattara ilimi da bayanai ayanar gizo a yanzu kamar wikipidiya, kuma miliyoyin ɗalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga manhajar a kullum.
An ƙaddamar da shafinWikipidiya ne a ranar 15 ga watanJanairun shekara ta 2001,Jimmy Wales tare daLarry Sanger ne suka haɗa gwiwa wajen samar da shafin. Suka sanya mata suna ta hanyar hade kalmarwiki daencyclopedia. A farkon ƙirƙirar shafin an kafa tane daTuranci kadai amma daga baya sanadiyar karɓuwa da shafin yayi ne yasa ake samar da ƙarin Harsuna akai-akai har zuwa yanzu. A halin yanzu akwai maƙaloli sama da 6,713,721 a sashen Wikipidiya naTuranci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne shahara da tarin maƙaloli. Ayanzu akwai sama da maƙaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka sama da 301, sannan shafin yana samun masu ziyara mabanbanta sama miliyan 500, adadin duka masu ziyara sunkai sama da biliyan 18 ko wanne wata tun daga watanFabrairu na shekara ta 2014.
A sashenHausa na wikipidiya kuma akwai maƙaloli sama da dubu 53 ya zuwa watan Janairu a shekara ta 2025.[6] duk da yake sashen yana da ƙarancin masu bayar dagudunmuwa amma a hankali sashen yana ƙara bunƙasa cikin gaggawa.