Turmi wani abu ne daga cikin ka yan aikin gida wanda aka sassaƙa shi domin a dinmga daka da shi, ana sassaƙa shi daga itace masu karfi. Turmi ya kasu kashi biyu, Turmin da aka sassaƙa da Turmin ƙarfe, Turmin da aka sassaƙa shi ne Wanda ake aikin gida da shi, kamar daka da jajjagenkayan miya da dai sauran su. shi kuma Turmin karfe shi ne Turmin da ake daka magani a cikin sa ko kumaTurare, kamarkwalli,sabulu da sauransu.
wani tsohon turmi da ake jima dashi
Ana kuma amfani da turmi wajen daka, kamar irin su dakanFura irinFulani haka, har ma da dakantuwo wani lokacin. Ana kuma dakanmagani da shi, ana yin jajjagenkayan miyamisali ba sai an kai markade ba, ana kuma dakan ƙasar gini da dai sauran su. Kusan kowane gida akwai turmi saboda amfanin turmi kodaamarya za'a kai sai an kuma haɗa ta da turmi (sai an siya mata turmi).Turmi shine TiloTurame kuma shine jam'i.[1]
Shi Kuma Turmi baya yiwwuwa ayi amfani dashi dole saidaTaɓarya itamaTaɓarya sassaƙa ta akeyi kamar yadda ake sassaƙaTurmi. Akan ma mutum lakabi da turmi sha daka idan ya shahara sosai.[2]