Wannan mukalar bata daReference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar daReference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
.
Siyasa hanya ce damutane ke bi wajenrayuwa a hade, ko a tare, ko akungiyance cikin manufa daya. Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da mabam-bantan ra'ayoyi,kabilu daaddinai, abirane dakasashe. A manyan kashashe mutane da dama kan ɗauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa. Wadannan mutane kuma su ake ƙira daYan'siyasa. Yan-siyasa da kuma wadansu mutane kan hadu domin samar daGwamnati da tafiyar a tare. Karatun tafiyar da gwamnati ajami'a ana kiranshi daIlimin kimiyar siyasa da (turanciPolitical Science, ko Political Studies).
Siyasa al'amari ne da yake kunshe da manufofi da kuma tsare-tsare.
A ma'anar ko yausheSiyasa na nufin hanyar da kasashe ke bi domin aiwatar da mulki ko gwamnati, da kuma hanyar da gwamnatoci ke bi wajen aiwatar da dokoki. Ana kuma yin siyasa a wasu guraren kamar Kamfanoni, kungiyoyi, makarantu, masallatai da majami'u.