Masu sarautar saudiyaYarima Named bin Abdullahi bin Saudi bin xudeyr na saudiyya kenansaudi
Saudi Arebiya koSaudiyya: ƙasa ce da take nahiyarGabas ta Tsakiya a Duniya.
Ƙasar Saudiya ta kasance ne a nahiyar Asiya, ta kuma kasance fitacciyar ƙasa a duniya musamman ta ɓangaren addinin musulunci, kasantuwar addinin musulunci ya zo ne ta hannun Annabi Muhammad (S. A. W) da yake a wannan yanki, hakama a tattalin arziki,Allah ya azurta ƙasar da ɗinbin arziki da ma'adinai musamman arzikin man fetur. Ƙasar Saudiyya ta kasance ita ce ƙasar da ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a faɗin Duniya. Lallai ƙasar Saudiya ta kasance ƙasa ce wacce take daSahara.
Ƙasar na da mafi yawan bishiyoyinDabino, kuma su kan noma alkama daInabi kuma suna ɗaya daga cikin manyan ƙasashe wurin noman gyaɗar itacenAlmond wanda ake mai na gashi, da kumaMadaran Almond, haka kuma kasar Saudiya na noman itacenzaitun watuOlive a turanchi da kuma sauran su. Harshen yan kasar ta kasanceLarabci, wanda shine yaren kasar, kuma musulmai daga sassa daban daban na duniya sukan je domin su aiwatar da ibadun su a kasar, kamar aikin Hajji da Umra.[1]
Saudiya kasa ce mai tsarki kuma baya hallata mutum yaje yayi abun da yaga dama ciki suna da dokoki da tsare-tsaren su ba kamar sauran ƙasashe ba.[2]
saudi meccatutar sauditutar saudisaudi, omanmanunin saudi
Dakinka'aba na garinMakkah mai AlfarmaMusulmai masu aikin hajji a masallaci a kasar saudiyya
Kasar saudiya kasa ce ta musulunci, wanda a cikinta ne aka aiko annabin karshe, wato Annabi Muhammad(tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi). Duk shekara miliyoyin Mutane ne suke kai ziyara kasar dagakasashen duniya daban-daban domin aikin hajji mai alfarma da Umrah. Haka kuma kasar Saudiya Arabiya ba a barta a baya ba wurin fannin tsaro ya kasance 23 cikin 145 daga cikin kasashen da aka yi la'akari da su wurin gwajin.karfin sojoji ta duniya na shekara-shekara. Kuma kasar Saudi Arabiya na daya daga chikin manya manyan kasashen dake fitar dadanyen mai. Kuma suna chikinKungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur WatuOPEC.