Rabīʿ al-ʾawwal (Larabci ربيع الأوّل) shi ne wata na uku a watannin shekara naMusulunci. A cikin wannan watanMusulmai da dama kan yi bukukuwan Maulidi (bikin murnar haihuwar fiyayyen halittaAnnabiMuhammad S.A.W).Musulmai mabiyaSunnah sun hakikance da Ranar 12 ga watan aka haifiAnnabiMuhammad (S.A.W), yayin da mabiyaShi'a suka hakikance da ranar 17 ne da Asuba aka haife Shi. Annabi bai yi bikin Maulidinsa ba da kansa, sai dai ya yi nuni aHadisi game da Musulmai su rinkaazumi a ranar kowacce Litinin domin ita ce ranar da aka haifeshi. Duka dai Musulmai na girmama wannan watan.[1]
Musulmai aIndiya dauke da korayen tutoci na bikin Maulidi
Babu wani hakikanin tarihi game da ainahin ranar ko kwanan watan da aka haifi Annabi Muhammad (s.a.w) sai dai shi din Annabin ya yi nuni da an haife shi a ranar Litinin ne amma bai taba fadan kwanan watan ba. Amma masu bikinMauludi na daukar ranar 12 ko 17 a matsayin ranar haihuwar Sa. Inda suke gudanar da bukukuwan a sassa daban daban na kasashe da dama na duniya.[2]