(Poliomyelitis), a harshen Turanci watoCutar Polio ko kumaCutar shan inna, cuta ne da ake iya dauka daga wani ta dalilin kwayoyin cutar polio (poliovirus).[1] Kusan kaso 75% na cutar basa nuna alamomin cutar;[2] ana iya samun kananan alamomi kamar ciwon makoshi da zazzabi; a yawancin lokuta alamomi kan tsananta kamarciwon kai, ciwon wuya, da kumaParesthesia.[1][3] Wadannan alamomi sukan wuce a tsakanin mako daya ko biyu.[1] Alamar gama-gari itace shanyewar sashin jiki na dundundun, da kuma mutuwa a wasu lokuta idan tayi tsanani.[1] Ana iya samun alamomin cutar (post-polio syndrome) shekaru kadan bayan warke daga cutar, da kuma habakar karancin karfi gabbai irin wanda mutum ke fuskanta yayin kamuwa cutan.[4]
Cutar shan inna na faruwa ne hakanan ne ga dan-Adam.[1] Tana da saurin yaduwa matuka, kuma tana yaduwa daga wani zuwa wani ta hanyar cudanya ta baki ko fuska[1][5] (misali a dalilin gurbataccen muhalli, ko kuma ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ke dauke da kashin dan-adam), ko kuma ta hanyar cudanya ta baki da baki.[1] Wadanda suka kamu da cutar suna iya yadata ga sauran mutane har tsawon makonni shida ko da ace basu fara nuna wasu alamomi ba.[1] Ana iya gano asalin cutar ta hanyar nemo kwayar cutar a cikin kashin mutum ko kuma nemo kwayoyin halitta masu fada da kwayoyin cuta acikin jini.[1]
Polio
Poliomyelitis (kwayoyin cutar shan inna) sun wanzu na tsawon shekaru dubunnai da suka gabata, tare da nuna cutar acikin zanukan zamunan baya.[1] Wanda ya fara gano wannan cutar wani masanin magunguna ne bature dan IngilaMichael Underwood a matsayin cuta mai rudarwa acikin shakarar 1789,[1][6] sannan kuma an fara gano kwayoyin cutar da ke janyo cutar a shekarar 1909, wanda wani mai binciken kwayoyin kariyar jiki dan kasar AustriyaKarl Landsteiner.[7][8] An samu manyan barkewar cutar acikin karni na 19 a kasashen Turai da Amurka,[1] sannan acikin karni na 20, cutar ta zamonta cuta mafi tada hankali acikin cututtukan da ke kama kananan yara.[9] Bayan gano rigakafin cutar acikin shekarun 1950s, cutar shan inna ta ragu acikin sauri.[1]
Wannan Muƙalarguntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iyagyara ta.
↑1.001.011.021.031.041.051.061.071.081.091.101.111.12Estivariz, Concepcion F.; Link-Gelles, Ruth; Shimabukuro, Tom (2021). "Chapter 18: Poliomyelitis". In Hall, Elisha; Wodi, A. Patricia; Hamborsky, Jennifer; Morelli, Valerie; Schillie, Sarah (eds.).Epidemiology and Prevention of Vaccine-Preventable Diseases (The Pink Book). (14th ed.). Centers for Disease Control and Prevention (CDC, US). Archived from the original on 17 March 2022.
↑"Disease factsheet about poliomyelitis".European Centre for Disease Prevention and Control. European Centre for Disease Prevention and Control. 26 March 2013. Retrieved 12 April 2023.
↑"Poliomyelitis: Key facts". World Health Organisation. 22 July 2019. Archived from the original on 18 April 2017.
↑"Post-Polio Syndrome Fact Sheet". NIH. 16 April 2014. Archived from the original on 29 July 2011. Retrieved 4 November 2014.
↑CDC (29 March 2022). "What is Polio?".Centers for Disease Control and Prevention. Retrieved 24 April 2022.
↑Underwood, Michael (1789).A Treatise on the Diseases of Children. Vol. 2. London, England: J. Mathews. pp. 53–57.
↑Daniel TM, Robbins FC, eds. (1999).Polio(1st ed.). Rochester, NY: University of Rochester Press. p. 11. ISBN9781580460668. Archived from the original on 17 June 2016.
↑Landsteiner, Karl; Popper, Erwin (1909). "Übertragung der Poliomyelitis acuta auf Affen"[Transmission of Poliomyelitis acuta to monkeys].Zeitschrift für Immunitätsforschung und experimentelle Therapie [Journal for Research on Immunity and Experimental Therapy] (in German).2 (4): 377–390.
↑Wheeler DS, Wong HR, Shanley TP, eds. (2009).Science and practice of pediatric critical care medicine. London: Springer. pp. 10–11. ISBN9781848009219. Archived from the original on 17 June 2016.