![]() | |
---|---|
Emirate(en)![]() | |
Bayanai | |
Farawa | 1898 |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | Kwara |
Mazaunin mutane | Pategi |
Masarautar Patigi Jiha ce ta gargajiya ta Najeriya wacceIdrissu Gana na ɗaya ya kafa ta a shekarar 1898, sunan patigi yana nufin 'karamin tudu ' Masarautar dake cikin ƙaramar hukumar pategi tajihar kwara kuma babban birninPategi.[1]
Idrssu Gana ne ya kafa Masarautar wanda a shekarar 1898, ya jagoranci wata ƙungiya (Kede), wata ƙungiya ce ta ƴan ƙabilarNupe daga Bida a yakin da Turawan Mulkin Mallaka suka yi, kuma mutanen Nupe da yare naYarbawa ne ke zaune a masarautar. daga cikin mutanen akwai manoma masu fatauci da masunta.[ana buƙatar hujja]
Masarautar duka mutanen Nupe ne a cikinta kuma tana gudanar da bikin kwale-kwale da aka fi sani daBikin Pategi Regatta wanda aka yi akasari a yankin kogin Neja a bakinTekun Patigi. Taron kwale-kwale na tarihi da kuma yawon buɗe ido da FarfesaIdrissu Aliyu ya ce majalisar gargajiya ta Masarautar ne suka kafa ta a shekarar 1949 a hannun shugaban majalissar guda biyu, Ahman Pategi da Etsu Umaru Bologi I, an fara gudanar da bikin-ne a shekarar 1952, bakin kogin Niger Kwara da Niger Kogi. Bikin wanda ya ƙunshi tseren kwale-kwale ko kwale-kwale ya haɗa da baje kolin a Nijar Gbaradogi da ke gabar kogin yamma, Masarautar kuma ta yi bikinranar al'adun Nupe da ake gudanarwa duk shekara a watan Yuli kuma ya kasance tarihin mamaye yankin Nupe gaba ɗaya kan Turawan mulkin mallaka.[2][3]
Sunan sarki a pategi ana kiransa da Etsu na Patigi. Etsu na Patigi na yanzu shine AlhajiUmar Bologi II.[4][5] Jerin sarakunan gargajiya na masarautar Patigi da aka fi sani da Etsu Patigi da aka kafa a ƙarni na 16:[6][7]