Joseph Michael Yobo (an haife shi a ranar shida 6 ga watan Satumban shekara ta alif ɗari tara da tamanin 1980A.c), tsohon ɗan wasan ƙwallonƙafa ta Nijeriya ne wanda ya yi wasa a matsayin mai tsaron baya . Ya kasance kyaftin din kungiyar [kungiyar kwallon kafar Najeriya|kwallon kafa ta Najeriya]] har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga kwallon kafa a duniya a watan Yunin a shekarata 2014, kuma shi ne mai rike da kambun tarihin Najeriya. A watan Fabrairun shekarata 2020, Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Najeriya ta kungiyar kwallon kafar Najeriya|nada shi mataimakin kocin kungiyar Super Eagles]] .
Yobo ya bar Najeriya ya koma Standard Liège a shekarar 1998. Ya fara zama na farko a kungiyar a shekara ta 2000, sannan ya ci gaba da bayyana har sau 46. A shekarata 2001, Marseille ce ta saye shi.
Yobo tsohon dankwallon Najeriya ne, wanda ya buga wasanni 101 kuma ya wakilci Super Eagles a Kofin Duniya na FIFA uku da kuma Kofin Kasashen Afirka shida.
A ranar 12 ga Fabrairun 2020, Yobo ya zama Mataimakin mai bada horo naSuper Eagles ta Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya bayan wani gajeren taro da aka gudanar aAbuja . An nada shi mataimakin koci don maye gurbin Imama Amapakabo .
A shekarar 2010, bayan wata ‘yar gajeriyar soyayya, Yobo ya auri tsohuwar mai riƙe da muƙamin MBGN Adaeze Igwe inda aka yi shagalin bikin su aJos . Ma'auratan sun yi aure a wani ƙaramin mahimmin biki kusan watanni uku bayan haduwarsu a watan Disambar 2009. Ma'auratan sun yi haifi jariri mai suna Joey Yobo a watan Afrilun 2010.
A shekarar 2007, Yobo ya kafa Gidauniyar Sadaka ta Joseph Yobo, don taimakawa kananan yara marasa galihu a Najeriya. Tun daga ranar 18 ga watan Yulin 2007, ya ba da kyaututtukan tallafin karatu a sama da ɗalibai 300 daga matakin firamare zuwa matakin jami'a. Asali Yobo ya fara makarantar koyon wasan kwallon kafa ne a yankin Ogoni na Najeriya. Ya kuma jagoranci sansanonin kwallon kafa aLegas .
Yobo ya bar Najeriya ya koma Standard Liège a shekarata (dubu daya da dari tara da chasa'in da takwas) 1998.Ya buga wasansa na farko a shekarata (dubu biyu) 2000, kuma ya ci gaba da bayyana sau (arba'in da shida)46.A shekarata (dubu biyu da daya) 2001, Marseille ta saya shi.