«Siyinqaba» «We are a fortress» «Ние сме укреплението» «A royal experience» «Մենք ամրոց ենք» «Wir sind die Festung» «Som la fortalesa» «'Da Ni'n Gaer!»
Eswatini koSwaziland bayan 2018 (daSwati:Umbuso we Swatini; daTuranci:Kingdom of eSwatini) ƙasa ce wacce babu wani teku da haɗu da wani yankin ta, da ke a KudancinAfirka. Ta haɗa iyaka daMozambik daga arewa maso gabas, da kumaAfirka ta Kudu daga arewa, yamma, kudu, da kudu maso gabas. Tana da ƙarancin faɗin ƙasa kimanin 200 km (120 mi) daga arewa zuwa kudu, da kuma kilomita 130 km (81 mi) daga gabas zuwa yamma, Eswatini tana ɗaya daga cikin mafi ƙananan ƙasa a Afurka, duk da haka, yanayin sararin samaniya na ƙasar ya bambanta, yana juyawa daga sanyi irin na tsaunuka zuwa zafi da rani irin na sauran yankunan kwari.
Eswatini tana da yawan fili kimanin kilomita arabba'i 17,364. Eswatini tana da yawan jama'a kimanin 1,093,238, bisa ga jimillar 2017. Mafi yawancin jama'arta sun kunshiKabilar Swazi. Babban birnin eSwatini shineMbabane.