Jihar Delta Jiha ce dake kudu maso kudancinNajeriya. Jihar ta samo sunanta ne daga yankin Niger Delta[1] - wacce mafi akasarinta ke cikin jihar. An kirkiri jihar ne daga yankin tsohuwarJihar Bendel a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Agusta, shekara ta dubu daya da dari tara da cassa'in da daya 1991. Jihar Delta ta hada iyaka da JiharEdo daga arewa, daga gabas kuma da jihohinAnambra daRivers, sannan daga kudu kuma da JiharBayelsa, sannan daga yamma kuma da yankinBright of Benin,[2] wacce ta mamaye a kalla kilomita dari da sittin 160 na yankin ruwayen garin. An kirkiri jihar ne daga farko da kananan hukumomi Sha biyar 15 a shekarar 1991, sai daga baya aka kara ta koma sha tara 19, sannan daga bisani kuma zuwa kananan hukumomi ashirin da biyar. Babban birnin Jihar itaceAsaba wacce ke yankin Kogin Neje daga karshen arewa maso Gabashin jihar, a yayin daWarri ke taka rawa a matsayi cibiyar kasuwancin daga kudu maso yammacin gabar ruwan jihar.
Acikin jihohi talatin da shida 36 da ke a kasar Najeriya, Jihar Delta ita ce ta ashirin da uku a fadin kasa kuma ita ce ta sha biyu 12 a yawan jama'a da mutane kimanin miliyan biyar da dugo shida 5.6 a bisa kiyasin kidayar shekara ta dubu biyu da sha shida 2016.[3] Jihar, ta fuskar yanayin kasa ta kasu zuwa Mangrove na Afirka ta tsakiya daga yankin ruwa na kudu maso yamma da kuma dajika masu kwari irin na Najeriya wacce ta mamaye daukacin jihar da kuma dazuka masu fadama daga kuryar Kudancin jihar. Wani muhimmi al'amari a jihar sune gabarKogin Neja da rassan sa da kuma Sauran ruwayen kamanKogin Forçados wanda ke gudana daga yammaci da gabashin iyakokin Jihar Delta kuma ya fada Kogin Neja, da kumaKogin Escravos wacce ke kwarara taWarri sa'annan kuma yawancin yankunan ruwayen garin na dauke ne da dimbin dananan rafuka wadanda suka samar da akasarin yammacinNiger Delta. Mafi akasarin dabbobi da ake samu a yankin sun hada da; kadoji, tsuntsaye Parrot, nauyin kerkeci naAfrican fish eagle, da birai na Mona, da kuma damisan Afirka, da kuma nau'in biran chimpanzee na Najeriya da Kamaru.[4][5]
Logon jihar Delta
Jihar Delta ta yau ta kunshi kabilu da dama na tsawon lokaci wanda suka hada dakabilar Isoko daHarshen Eruwa wanda suka mamaye yankunan tsakiyar jihar;kabilar Ukwuani daga gabas; yayindakabilar Ika,Olukumi da kumaOzanogogo suka mamaye arewa maso Gabashin jihar; Anioma daga arewa maso yamma; kabilu Ijaw, Itsekiri, Urhobo, da Uvwie daga yankin arewa maso yamma. Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, yankin Jihar Delta ta yau ta kasu zuwa masarautu masu mulkin kansu kamar suMasaraWarri daMasarautar Agbon kafin su zamo yankin mulkin mallakar Turawa na Oil River Protectorate a shekara ta dubu daya da dari takwas da tamanin da hudu 1884. A shekara ta dubu daya da dari tara 1900, Turawa sun hade yankin (wato Niger Coast Protectorate) da yankin Mulkin Mallakan Turawa na Kudu wacce daga bisani ta zamo Najeriya ta Burtaniya. Duk da haka, Turawan mulkin mallaka basu gama samun cikakken iko akan yankin ba sai a shekarar 1910 a dalilin rikice-rikicenEkumeku Movement. Kamar yadda aka sani, acikin Jihar Delta akwai yankunan da ke karkashin ikon kasar Faransa wanda turawan Burtaniya suka sake wa FaransaYankunan Forcados da Badjibo a tasakanin shekara ta 1903 zuwa shekara ta 1930.
Bayan samun 'yancin kai, yankin Jihar Delta ta yau na daga cikin yankinJihar Yammacin Najeriya bayan samun 'yancin Najeriya, har zuwa shekarar 1963, lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta fada karkashinYankin Yamma ta Tsakiya ta Najeriya. Haka zalika a shekarar 1967 ne yankin Inyamurai watau tsohuwarYankin Gabashin Najeriya ta suka so kafa sabuwar kasarBiyafara kuma suka kaiwaYankin Yamma ta Tsakiya hari tare da nufin kame JiharLagos kuma su kawo karshenYakin amma an hanasu kuma an kora su na dan lokaci amma daga baya suka kame yankin (harda Jihar Delta ta yau) suka rada mata sunaTarayyar Benin. Acikin wannan hali, anyi kazamin barna a tsakanin sojojin Biyafara da kuma mutane mazauna yankin Jihar Delta ta yau, tare da kisan gilla da 'yan Bifara ke yiwa 'yan ainihin kabilunHausa,Urhobo da kumaKabilar Ijaw; haka zalika, sojojin Najeriya a yayin amsar jihar sun gudanar daKisan kiyashin Asaba ga mutanen asalin yaren Igbo. Yakin ya kawo karshe kuma an mayar daYankin Yamma ta Tsakiya cikin Najeriya, har zuwa shekarar 1976 lokacin da aka sauya mata suna zuwaJihar Bendel. A shekarar 1991, an raba Jihar Bendel, arewacinta ta zamoJihar Edo, yayinda kudancinta ta zamo Jihar Delta.[6]
Tattalin arzikin jihar[7] sun ta'allaka ne akan samar da man fetur da gas, a matsayin daya daga cikin muhimman jihohin dake samar da man fetur a Nejeriya.[8] Kadan daga cikin muhimman masana'antun sun hada da noma yayin da jihar ke samar da isashhenmanja,doya darogo dangane da kamun/kiwon kifi da samar da fure. Dangane da albarkacin man fetur, jihar ita ce ta hudu acikinJerin Jihohi Najeriya dangane da Ma'aunin Cigaban Jama'a a kasar; duk da haka, rikice-rikice tsakanin kamfanonin mai da kuma mutanen garin sun kawo cikas dangane da cin hanci da rashawa wanda suka janyo rashin ci gaba musamman a yankunan da ake hako man.[9][10]
Jihar na da fadin fili na kimanin 18,050 km2 (6,970 sq mi) wanda fiye da kashi 60% doron kasa ne. Jihar na nan a lambobin wuri a kalla 5°00' da 6°45' E da kuma 5°00'da 6°30' N.[11] Tana nan aYankin Yamma ta Tsakiyan Najeriya kuma ta hada iyaka da JiharEdo daga arewa, daga gabas kuma da jihohinAnambra da Rivers, sannan daga kudu kuma da JiharBayelsa, sannan daga yamma kuma da yankinBright of Benin wanda ya mamaye kilomitoci 160km na yankin ruwan jihar. Jihar Delta na kan kwari ne ba tare da tudu ko guda ba. Akwai yankunan ruwa da dama a jihar wadanda suke hade da koramu wanda suka samar da yankinKogin Niger Delta.[12]
An kirkiri Jihar Delta ne daga tsohuwar Jihar Bendel a ranar 27 ga watan Augustan shekara ta 1991.[13] An samar da jihar ne a sanadiyyar riritawa don samar da jiha ta daban da mutanen ainihi na Gundumar Delta suka yi.[14] Haka zalika akwai bukata ta sabuwar jihar mai suna "Jihar Anioma" wanda ta hada da yankunanAsaba daAgbor na yankin tsohuwar Yankin Yamma ta Tsakiya.[15] Shugaban kasa soja na lokacin Gen.Ibrahim Babangida ya zaba Jihar Delta tare daAsaba wata shahararriyar birnin a yankin arewa maso yammacinNiger a matsayin babban birnin jihar. Jihar Delta ta kasance a da daga cikin Yankin Yamma ta Tsakiya daga shekarar ta 1963 zuwa ta 1976, daga bisani kum Jihar Bendel a tsakanin shekara ta 1976 zuwa shekaran ta 1991. Sunan "Bendel" ta samo asali daga tsaffin gundomomin Benin da Delta na Yankin Yammacin Delta don nuna muhimmancin gundumomin guda biyu (Benin da Delta).[16]
KabilarUrhobo-Isoko na da mafi rinjayen mutane kuma a yanzu akwai mutum akalla miliyan 2.6 a jihar.[18] Gungun yaruka na Iboid na jihar sun hada daMutanen Anioma (mutanen gari mai kyau).[19] kabilar Itsekiri na amfani da yare mai kama da yarbanci amma yana da alaka da al'adunkabilar Edo na Jihar Edo, hadi da yarukan Urhobo da Ijaw. Kabilar Ijaw mutane ne masu alaka da makwabtansu na Jihar Bayelsa,[20] yayinda yaren Olukumi suka fara bacewa ta fuskar al'ada da yare,[21] a dalilin cudanya da wasu harsunan.
An zabiArthur Okowa Ifeanyi, dan takara a karkashin jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan Jihar Delta a cikin watan Afrilun 2015.[22] Mataimakinsa shi neKingsley Otuaro.[23] Jihar na da mazabu uku (Arewa, Kudu da Tsakiya). Sanatocin da aka zaba a zaben shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2013 suneJames Manager,Arthur Okowa Ifeanyi da kuma Emmanuel Aguariavwodo wanda ya maye gurbinPius Ewherido wanda ya rasu a shekara ta 2013 a Asibitin Tarayya dake Abuja.[24] An zabi Chief Ighoyeta Amori a zaben shekara ta 2015, amma an soke nasa zaben kuma an rantsar da SanataOvie Omo-Agege a matsayin sanata mai wakiltar Delta ta Tsakiya.[25][25]James Manager ya koma kujerarsa kuma an zabiPeter Nwaoboshi a matsayin sanata mai wakiltar Arewacin jihar.
Jihar Delta tana da adadinKananan hukumomi guda ashirin da biyar (25), an kawo su a jere a jadawalin dake kasa tare da kasafin kidayar shekara ta 2006:
Akwai ma'adanai iri-iri a jihar kamar su:industrial clay,silica,lignite,kaolin,tar sand, duwatsu na ado,limestone da dai sauransu.[35] Ana amfani da wadannan ma'adanai a ma'aikatu wajen hada ceramic, kwalba, gilasai, alli, wayoyi, da makamantansu.[36]
Har ila yau, akwai tarin arzikin man fetur a Jihar Delta, kuma tana daya daga cikin muhimman garuruwan da ke samar da kayan da ake hadawa daga man fetur a Najeriya. Tattalin arzikin jihar sun ta'allaka ne matuka a wajen cinikin man fetur.
A Jihar Delta, akwai wuraren tarihi, al'adu da zamantakewa na siyasa, wuraren bude idanun da ke jan hankalin 'yan kallo daga ko'ina a fadin duniya.Wasu daga cikin wadannan wurare sun hada da:[25]
Fadar Nana (The Nana's Palace) wanda ChiefNana Olomu na Ebrohim ya gina. Ya shahara a karni na 19, kuma dan kasuwa ne na garin da yayi hulda da turawa. Daga baya huldar ta baci. An mamaye daga baya (ba tare da anyi fada ba) sai suka koma kasar Ghana. Abubuwan da ya bari sun hada da katafaren fadar sa dake gidansa.[Ana bukatan hujja]
Rafin Ethiope iwanda ake ikirarin cewa shine ruwa mafi zurfi acikin garuruwan Afurka (zurfi 176 km). Mabubbugar ruwan na kusa da wani katafaren bishiya silikin auduga dake Umuaja a karamar hukumar Ukwuani sannan tana kwararar ta kananan hukumomin jihar source is at the foot of a giant silk-cotton tree at Umuaja in Ukuami sannan su kwarara zuwa Sauran yan kananan hukumomin jihar. Wurin bauta ne na addinin gargajiya na Olokun sannan kuma wurin bautar na mabiya addinin Agbe.[62]
Yankin Bible na Arayawanda ke dauke da kwafi na Littafin mai tsarki na Bible. An yarda da cewa Littafin Bible ya sauka a wannan yankin cikin al'ajabi daga sama a cikin watan Augusta, 1914. Littafin na bible ya sauko ne acikin wani jikakken doya daga ruwan sama amma bai jike ba. Yankin na janyo dubunnan mabiya addinin kirista duk shekara.[63]
Demas Nwoko Edificewanda aka gina da kayan aiki na gargajiya, tsari da salon gini na cigaban mutanen Igbo wandaDemas Nwoko wani mai zane, ma gini kuma mai fasaha na duniya daga garin Idumuje-Ugboko, a karamar hukumar Aniocha ta Arewa, Jihar Delta.[64]
Gidan shakatawa na "Mungo Park House" wanda a yanzu Gidan Tarihi ne na Kasa, aAsaba.Royal Niger Company suka gina gidan a shekara ta 1886 kuma turawa sunyi amfani dashi a matsayin hedikwatan, gidan sojojin, hedikwatan gidan Gwamnatin turawa, gindin RNC, da kuma mazauni Gundumar Birni a lokuta daban daban.[65]
GadarNiger Bridge wacce ta hade Jihar Delta (daga yammacin Najeriya) zuwa yankin Gabashin Najeriya. Wuri ne mai kyawun gani wacce aka kammala a shekara ta1995 akan kudi ki manin miliyan £5. An lalata ta a lokacin yakin basasar Najeriya, amma daga bisani an gyara ta.[66]
Lander Brothers Anchorage, Asaba wanda aka gina don tunawa da Turawan Birtaniya da suka fara ziyartar Najeriya. Babban gindin na dauke da gidan tarihi, makabarta, da zane da rubuce-rubuce da dama. Akwai irin jirgin 'Yan uwan suka yi amfani dashi.[Ana bukatan hujja]
Falcorp Mangrove Park
Makabartar ta Musamman na Masarautar Warri makabarta ce da ta kai kimanin shekaru 512 kuma tana matsayin makwancin sarakunan Masarautar Warri. Akwai shuka da aka gina a kowanne kabari.[67]
Stephen Keshi, tsohon ma tsaron baya, tsohon coach na super eagles[92]
Festus Keyamo, Lauyan Najeriya kuma[93] member na ƙungiyar Senior Advocate of Nigeria SAN
Lynxxx, mawaki, dan kasuwa kuma jakada kamfanin Pepsi na farko a Najeriya[94]
Rosaline Meurer, 'yar wasan kwaikwayo na Najeriya haihifaffiyar Kasar Gambiya[95]
Richard Mofe-Damijo, ƙwararrun dan wasan kwaikwayo na Najeriya, marubuci, furodusa, lauya kuma tsohon kwamishinan al'adu da bude idanu na Jihar Delta.[96]
Collins Nweke, mutum na farko da ba Haifaffun Kasar Belgium ba daka fara zaba a ofishin siyasa a yankin West Flanders na Belgium[97]
Ngozi Okonjo-Iweala, masanin tattalin arziki, kuma ƙwararren masanin cigaba na kasa da kasa, na kamfanin Boards of Standard Chartered Bank, Twitter, Global Alliance for Vaccines and Immunization, da kuma African Risk Capacity[107]
Bruce Onobrakpeya, wanda ya lashe lambar yabo na 2006 UNESCO Living Human Treasure Award, amintacce a Jami'ar Western Niger Delta University[Ana bukatan hujja]
Gamaliel Onosode, technocrat dan Najeriya, dan siyasa kuma tsohon dan takarar shugabancin Kasar Najeriya[114]
Zulu Sofola, marubuciya ta farko da aka fara wallafa littafin ta a Najeriya kuma 'yar wasan drama, farfesan mace ta farko a fannin tsara wasannin a nahiyar Afurka[125]
Ojo Taiye, mawakin fasahan Najeriya, wanda ya lashe kyauta a gasar Wild 2019 Annual Poetry Prize[126]
Abel Ubeku, Managing Director Bakin fata na farko a kamfanin Guinness Nigeria Plc[127]
Patrick Utomi, farfesan Najeriya akan political economy and management expert, Fellow of the Institute of Management Consultants of Nigeria kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya[128]
SenatorJames Manager Ebiowou, Dan siyasan Najeriya a mata in Sanata
↑"Niger Delta | geographical region, Africa | Britannica".www.britannica.com. Retrieved 2022-03-04.
↑"Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map".www.citypopulation.de. Retrieved 2022-03-11.
↑Lameed, GA (2009). "Potential impact on biodiversity in kwale's forest reserve by power plant establishments".African Journal of Food, Agriculture, Nutrition and Development.9 (30): 1878–1900.doi:10.18697/ajfand.30.1750.S2CID 240141039. Retrieved 19 December 2021.
↑Ijeomah, HM; Oruh, EK (2015). "Wildlife based business activities in Ogbe–Ijaw market of Delta state, Nigeria".Journal of Agriculture and Social Research.12 (2). Retrieved 19 December 2021.
↑"This is how the 36 states were created".Pulse.ng. 24 October 2017. Retrieved 15 December2021.
↑"Brief History of Delta State:: Nigeria Information & Guide".www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2022-03-11.
↑Akanbi, Festus (19 September 2021). "As Anambra, Kogi Join Oil-producing States".ThisDay. Retrieved 15 December 2021.
↑"Human Development Indices".Global Data Lab. Retrieved 15 December 2021.
↑Ebiri, Kelvin (17 November 2019). "Oil-producing communities reek of poverty despite over N10t 13% derivation".The Guardian. Retrieved 21 December2021.
↑Ebewore, Solomon Okeoghene (2020-01-01). "Rural Folks Perception of Suicide Drivers in rural communities of Delta State, Nigeria: Implications for Societal and Agricultural Security".Open Agriculture.5(1): 50–62.doi:10.1515/opag-2020-0005.ISSN 2391-9531.
↑"Brief History of Delta State:: Nigeria Information & Guide".www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2021-07-12.
↑Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State".Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
↑Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State".Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
↑Oseni, Z. I. (1987-01-01). "Modern Arabic and Islamic studies in Bendel state of Nigeria".Institute of Muslim Minority Affairs Journal.8 (1): 183–192.doi:10.1080/02666958708716027.ISSN 0266-6952.
↑Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State".Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
↑"Showcasing The Ijaw Culture and People of Bayelsa from South-South Nigeria - Courtesy The Scout Association of Nigeria".www.scout.org (in Arabic). Retrieved 2020-09-23.
↑Arokoyo, Bolanle (January 2020). "OLUKUMI DOCUMENTATION AND REVITALIZATION".ResearchGate. Retrieved 2020-09-23.
↑"Okowa wins Delta guber poll, Ogboru threatens suit".The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2015-04-14. Retrieved 2021-06-24.