Creedence Clearwater Revival, wanda aka fi sani daCCR ko kuma kawai Creedence, ƙungiyar mawaƙa ce ta Amurka da aka kafa a kasar El Cerrito, California . Kungiyar ta kunshi jagorar mawaƙa, jagorar guitarist, da kuma marubucin waƙoƙi na farko John Fogerty, ɗan'uwansa, dan wasan guitar Tom Fogerty, bassist Stu Cook, da kuma Doug Clifford. Wadannan mambobi kugiyar sun yi wasa tare tun a shekarar (1959), da farko a matsayinBlue Velvets sannan daga baya a matsayin Golliwogs, kafin su zauna a Creedence Clearwater Revival a shekara ta alif na dubu daya da dari tara da sittin da bakwan (1967). Lokacin da ƙungiyar ta fi yawa da samun cigaba da nasarori tsakanin shekarar (1969) da shekarar (1971) sun samar da goma sha huɗu a jere Top 10 singles (da yawa daga cikinsu sun kasance sau biyu A-sides) da biyar a jere Top Top 10 albums a Amurka, biyu daga cikinsu -Green River (1969) da Cosmo's Factory (1970) - sun hau kan jadawalin <i>Billboard</i> 200. Kungiyar ta yi a bikin Woodstock a shekarar (1969)
kasar New York, kuma ita ce babbar aikin farko da aka sanya hannu don bayyana a can.[1]
- ↑"Woodstock".history.com. History.com Editors. Retrieved24 March 2021.