| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Paterson(en) |
| ƙasa | Tarayyar Amurka |
| Karatu | |
| Makaranta | Duke University(en) |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a | orthopedic surgeon(en) |
| Kyaututtuka | gani
|
William James Mallon (an haife shi ranar 2 ga watan Fabrairu, 1952) likitan tiyatar kashi-(Orthopedic surgery) ne naAmurka, kuma tsohon ƙwararren ɗan wasan golf kuma mai jagoran wasannin Olympics.

An haifi Mallon aPaterson, New Jersey.[1] Ya yi karatu aJami'ar Duke kuma ya kammala karatun (magna cum laude) da sakamakon A.B. a fannin lissafi da Ilimin Kimiyyar abubuwa (physics). Yayin da yake Duke ya buga wasan golf na kwaleji kuma ya kasanceAll-American sau biyu, haka-zalika sau biyu ya na zaɓarfitattun 'yan wasan Kwaleji na Amurka kuma ya kasance ɗan takara sau biyu a gasar NCAA. Ya lashe gasa sama da 40 na wasan masu tasowa (amateur) da suka haɗa da; ƙwara biyu kowanne a gasarMassachusetts Amateur daNew England Amateur.[1] Har ila yau, ya lasheMiddle Atlantic Amateur sau ɗaya.[1]
A shekara ta 1975, Mallon ya zama ƙwararre.[1] Ya shigaPGA Tour bayan ya cancanci kammalaFall 1975 PGA Tour Qualifying Schooll.[1] Mallon ya buga wasanni tsawon kaka huɗu, daga 1976 zuwa 1979, an zabi mafi kayatarwa uku acikin 10 na wasanni da ya kammala.[2] Wasansa mafi kyayatarwa shi ne na 5 a 1977Joe Garagiola-Tucson Open. Mallon ya taka leda a gasar 1977 U.S. Open, kuma ya kasance sau biyu a cikin mutane 100 a jerin masu kudin gasar.

Bayan barin PGA Tour, Mallon ya koma Jami'ar Duke don karantar karatun likitanci a matsayin M.D. a 1984. Ya zauna a cibiyar kula da lafiya ta Jami'ar Duke tsakanin 1984 zuwa 1990 kuma yanzu shine Mataimakin Farfesa na Orthopedics kuma yana da nasa aikin na kashin kai. Mallon ya ƙware a ɓangaren haɗa/gyaran ko tiyatar kafaɗa da tiyatar gwiwar hannu kuma shi mabiyin ƙungiyar Cibiyar Nazarin Orthopedic Surgeons na Amurka, ne Hakazalika , memba naLikitan Jiki na Amurka da Jikin gwiwar hannu, inda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban wurin a shekarar 2012, kuma zai zama shugaba wurin a 2014, kuma memba. na majalisar shawara naCibiyar Kula da Magungunan Wasanni. Ya yi rubuce-rubuce sosai kan batun raunin wasanni kuma ya kasance editan likita na mujallarGolf Digest tun 1987. A baya Mallon ya kasance editan Arewacin Amurka naJaridar Shoulder and Elbow Surgery.
Har ila yau Mallon shi ne babban jami'i a tarihin gasar Olympics kuma ya rubuta littattafai 24 kan wannan batu. Ya kasance abokin haɗin gwiwa kuma daga baya shugaban kungiyar masana tarihi na Olympics na kasa da kasa kuma ya kasance mai ba da shawara kan tarihi ga kwamitocin shirya wasannin Olympics na Atlanta da Sydney. Mallon ya kasance mai ba da shawara kan ƙididdiga ga kwamitin Olympics na kasa da kasa kuma an ba shi lambar yabo ta Olympics a azurfa a shekara ta 2001 saboda hidimar da ya yi ga Olympics.