Lambar Bayelsaal'ummar BayelsaCikin kasuwar Swali a birnin BayelsaKogin bayelsaDaya daga cikin cocin jahar bayelsaAl adon balyalsa
Jihar Bayelsa jiha ce dake kudu maso kudancinNajeriya, tana nan a tsakiyar yankinNiger Delta.[1][2] An kirkiri Jihar Bayelsa[3] ne a shekarar alif dubu daya dari Tara da casa'in da shida (1996), kuma an cire ta ne dagaJihar Rivers.[4] Hakan yasa ta zamo daya daga cikin sabbin jihohinkasar. Ta hada iyaka daJihar Rivers[5] daga gabas, da kuma Jihar Delta daga yamma, indaTekun Atalanta[6] ta mamaye yankin kudancin jihar.[2]
Jihar Bayelsa nada fadin fili na kimanin kilomita 10,773kmaq, wanda yasa ta zamo jiha mafi karancin fili a Najeriya.[7] Kuma tana da yawan jama’a kimanin mutum 2,394,725, (kiyasin shekara ta 2016), wanda ya sanya ta jiha mai mafi karancin mutane. Babban birnin jihar, itaceYenagoa.Douye Diri ne gwamnan jihar a shekara ta 2022, mataimakin shi kuma shineLawrence Ewhrudjakpo.[8] Dattijan jihar sun hada da:Goodluck Jonathan,David Clark,Ben Murray Bruce,Emmanuel Paulker Izibefien daEvan Foster Ogola. A sanadiyyar kasancewarta a yankinNiger Delta, Jihar Bayelsa mamaye take da kogi da koramu, kuma kusan duka garin cikin ruwa yake, hakan ya jawo rashin cigabanta ta hanyar gina hanyoyi.[9]
Ana amfani da harshenIjaw a ko ina a jihar, tare da sauran harsuna kamarIsoko daUrhobo a tsaffin kyaukan jihar.
Bukukuwan bayelsa
Tana da kanan hukumomi 8: Ekeremor, Kolokuma/Opokuma, Yenagoa, Nembe, Ogbia, Sagbama, hi Brass da kuma Ijaw kudu. Bayelsa ta kasance gida gaMutanen Urhobo a karamar hukumarSagbama.[10]
A dalilin kasancewarta a yanki mai arzikin man-fetur watoNiger Delta, tattalin arzikin Jihar Bayelsa sun ta'allaka ne akan haka man-fetur da ma'aikatun tace su. YankinOloibiri Oilfield inda aka fara hako man fetur a Najeriya.[11] Sannan zuwa shekara ta 2015, an kiyasta cewa tana samar da kusan kashi 30-40% na man fetur din Najeriya.[12] Ana yiwa jihar lakabi da “Glory of all Lands” sannan ita ke da tafkin gas mafi girma a Najeriya (18 trillion cubic feet).[13] Duk da cewa jihar ta mallaki manyan rijiyoyin mai kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa, talauci yayi wa jihar katutu, hadi da gurbacewar muhalli[14] daga fesowar man fetur.[15][16]
Bayelsa na daga cikin jihohin kudancin Najeriya, jihar na nan a tsakiyar yankiNiger Delta. An cire Jihar Bayelsa dagaJihar Rivers, kuma tana daga cikin sabbin jihohin Najeriya.[18]
A karni na 20th, bukata na samar da sabuwar jiha da harshen Ijaw ke da rinjaye a yankinNiger Delta ya zamo sanannen abu. A tsakanin shekara ta 1941, zuwa ta 1956, an kafa kungiyoyi da dama dake goyon bayan samar da jiha naMutanen Ijaw a yankin Kudancin Najeriya.Isaac Adaka Boro, wani shahararren dan gwagwarmayar Ijaw a shekara ta 1960, wanda aka haifa aOloibiri yayi yinkurin ikirarin "Jimhoriyar Mutanen Niger Delta ("Niger Delta Peoples Republic") a shekara ta 1966.[20][21][22] Shugaban kasa na mulkin mallaka yaSani Abacha ne ya kirkiri Jihar Bayelsa dagaJihar Rivers a ranar 1, ga watan Oktoban, shekara ta 1966.[23] An samo asalin sunan ne daga haruffan farko na sunayen kananan hukumomin ta:Brass LGA (BALGA),Yenagoa LGA (YELGA) da kumaSagbama LGA (SALGA).[19]
A ranar 20, ga watan Disamban shekara ta 1999, ne sojojin Najeriya suka kaddamar da abinda aka fi sani daKisan Kiyashin Odi. Ana kokanta akan ainihin yawan mutanen da aka kashe, duk da cewa,Nnimmo Bassey, Babban Darekta na Hakkin Harkokin Muhalli, ya sanar cewa farar hula mutum 2500, ne suka rasa rayukansu.[24][25]
Dangane da zaizayar kasa a jihar a dalilin ma'aikatun man fetur, anyi zanga-zanga da dama kamar "Rise for Bayelsa" da akayi don inganta samar da ruwan sha a kananan yankuna. A cikin shekara ta 2019, ne, gwamnatin jihar Bayelsa ta fara neman gwagwarmayar samar da mafita dangane da matsalolin gurbacewar muhalli a jihar.[26][27]
Jihar na daya daga cikin jiha mafi albarkatun man fetur a Najeriya.[28][29] A dalilin haka, akwai yawaitar man fetur a jihar. Duk da cewa jihar tana da arziki mai, jihar na samun karancin kudi daga kasafin man fetur a dalilin rashin daidaituwa a tsarin kasafi daga gwamnatin kasar.[30]
Bayelsa na zagaye da ruwan kogi da kuma koramu. Yankunan jihar da dama suna kewaye ne da ruwa wanda haka yasa ba iya riskar su ta tituna. Akwai gandun daji na "Edumanom Forest Reserve" a jihar. Tun watan Yunin shekara ta 2008, inda aka ga birin chimpanzee na karshe itaceNiger Delta.[31] Sauran muhimman birane bayanYenagoa sun hada da;Akassa,Lobia, Amassoma (the home of theNiger Delta University), Eniwari,Ekeremor, Aliebiri, Peretoru,Twon-Brass, Egwema-Brass,Kaiama,Nembe, Odi,Ogbia, Okpoama,Brass, Oporoma, Korokorosei, Otuan, Koroama, Okolobiri, Obunagha, Ogboloma,Sagbama, Olugbobiri, Peremabiri, Ekowe, da kuma Swali.
Akwai kuma gininAkassa Lighthouse wanda ke nan tun shekara ta 1910.[32]
Asalin harshen da ake amfani dashi shineharshen Ijaw, tare da yaruka kamanKolukuma, Mein, Bomu,Nembe, Epie-Atisa, da kumaOgbia. Kamar dai a sauran jihohin Najeriya, Turanci ne harshen gwamnatin jihar.
Jerin harsunan Jihar Bayelsa dangane da kananan hukumomin LGA da ake amfani dasu:[33]
Wannan wani bakin hayaki ne da ke tashi a dalilin kona man fetur ba tare da ka'ida ba (ana kiransu a gargajiyance "wutan Kpo).[34] Wadannan mugayen sinadirai kan jawo rashin lafiya kamarCiwon huhu na daji, matsalolin fata, matsala ta mashakar iska da dai sauransu. Ana iya ganin sauran illolinta kamar gurbacewar iska, ruwa da kasa wanda hakan sun jawo mutuwan tsirrrai, mutane da kuma dabbobi.[35]
Wannan sanannen matsala ne a Jihar Bayelsa saboda tana kan gabarTekun Atalanta. Hauhawar igiyar ruwan teku ne muhimmin dalili na ambaliyar. Ambaliyar ta haifar da matsaloli ga al'ummomi da dama, dukiyoyi da kuma mutane. Kusan ko ina a Bayelsa na fuskantar matsalolin ambaliya, amma ambaliyar tafi tasiri a yankuna kamar Ekeremor, Ijaw ta kudu, Sagbama, Kolokuma/Opokuma da kuma Yenagoa wanda suke fuskantar barazanar duk shekara.[36] Rashin bin tsarin gine-gine na daga cikin dalilan dake assasa ambaliyar a Jihar Bayelsa.[37]
Wannan wani muhimmin al'amari ne dake kawo matsalar muhalli a Jihar Bayelsa a dalilin ayyukan kamfanonin man fetur a jihar. Zubewar mai na jawo illa ga gonaki, halittun ruwa da kuma mutane.[38] Kusan duk rana ana sanarwa Udengs Eradiri labarin zubar mai a Jihar Bayelsa, Niger Delta.
Kamar yadda yake fadi, a da zaka iya yin noma ka samu girbi mai kyau, ko kuma kaje kamun kifi ka kamo da yawa, amma yanzu zaka iya kwashe tsawon yini baka kama kifi ko guda daya ba.[39]
Wata matsala ta muhalli itace gurbacewar iska (Soot), wanda mafi akasarin mutanen Bayelsa na kukan cewa basu iya numfashi da kyau.[40]
Amma a shekara ta 2018, masu hannu da shuni sunyi kamfe mai taken "Save Rivers from this soot of death" wato a kiyaye koguna daga mutuwar Soot, a yankunan dake kewaye da ruwa.[41]
Owoye Andrew Azazi, Chief of Army Staff na (Nigeria), Chief of Defense Staff a lokacin mulkin shugabaOlusegun Obasanjo sannan kuma Mai ba wa shugaban kasa shawara akan harkar tsaron na shugaban kasaGoodluck Jonathan.
Edmund Daukoru, Ministan Najeriya na Jiha akan Makamashi kuma ya kasance Secretary General na Kungiyar Kasashe masu Fitar da Man Fetur a shekara ta 2006, HRM[47]
HonourableDouye Diri dan kasuwa, dan siyasa kuma mai zartarwa wanda ke wakiltar mazabarYenagoa/Kolokuna/Opokuma na 'yan majalisu.[49]
Tamara Eteimo wacce akafi sani da suna Tamara daga Angiama, karamar hukumar Ijaw ta kudu na Jihar Bayelsa. Mawakiyar R&B a Najeriya, marubuciyar waka kuma jaruma.[50]
↑"Nigeria's oil-rich Bayelsa State opens inquiry on spills".www.worldoil.com. Retrieved 2021-03-07.
↑"'This place used to be green': the brutal impact of oil in the Niger Delta".the Guardian. 2019-12-06. Retrieved 2021-03-07.
↑"Governor Diri, Odi School alumni raise funds for science laboratory project".Tribune Online. 2022-03-16. Retrieved 2022-03-23.
↑"Référence rapide des codes de la CITE-P et de la CITE-A dans la CITE 2011",Guide opérationnel CITE 2011, OECD, pp. 117–118, 2016-01-25,doi:10.1787/9789264248823-16-fr,ISBN9789264248830, retrieved 2021-09-10
↑19.019.1"Learn About Bayelsa State, Nigeria | People, Local Government and Business Opportunities in Bayelsa".Overview of Nigeria |NgEX. Retrieved 2018-07-29.
↑T., Akinyele, R. (2006).Isaac Adaka Boro : patriarch of minority activism in the Niger Delta. University of Lagos, Faculty of Arts.ISBN978-075-054-1.OCLC 752210539.
↑"Overview of Bayelsa State".Niger Delta Budget Monitoring Group. Retrieved 2021-03-09.
↑"Bayelsa – History & Culture – Bayelsa State Government". Retrieved 2022-02-11.
↑"Trade and human rights in the Niger Delta | Pambazuka News".www.pambazuka.org. Retrieved 2021-03-09.
↑"Odi massacre: Anyone with tribal marks on their chest was slaughtered, corpses littered everywhere –Bolou, former Bayelsa commissioner".Punch Newspapers. 2017-12-16. Retrieved 2021-09-10.
↑"Nigeria: Bayelsa state launches new inquiry into the environmental and human damage caused by oil spills in the Niger Delta".Business & Human Rights Resource Centre. Retrieved 2021-09-10.
↑"Nigeria's oil-rich Bayelsa State opens inquiry on spills".www.worldoil.com. Retrieved 2021-03-09.
↑"Bayelsa woos oil, gas, other investors".Vanguard News. 2019-04-23. Retrieved 2021-09-17.
↑"Bayelsa woos oil, gas, other investors".Vanguard News. 2019-04-23. Retrieved 2021-09-11.
↑Ikein, Augustine (2004). "Economic Development Agenda for Bayelsa State of Nigeria: An Advisor's Opinion" (PDF).Journal of Sustainable Development in Africa. Archived (PDF) from the original on 2009-01-07.
↑"Nigeria Biodiversity and Tropical Forestry Assessment" (PDF). USAID. June 2008. p. 76. Retrieved 2010-09-18.
↑"Since 1910, a Lighthouse in the Creeks".Folio Nigeria. Retrieved 17 August 2020.