Bayanau kalmomi ne da ke yin ƙarin bayani game da aikatau. Wannan bayani da suke yi shi ya ke fito da aikin a fili. Sukan faɗi gurin da aka yi aikin, lokacin da aka yi aiki ko kuma yadda aka yi, ake yi ko za a yi aiki.
Masana suka ce, kalma ce da ke yin ƙarin bayani game da aikatau a cikin jimla. Wato kenan, wannan kalma, ita ce fitilar da take haskaka aikatau a ganshi a fahimce shi.
Bayanau, kalmomi ne da ke yin bayanani game da aikatau a cikin jimla. Bayanau ya rarrabu zuwa bayanau na wuri wanda ke bayyana wurin da aka yi aiki, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aikin. Sai kuma bayanau na lokaci, wanda ke bayyana lokacin da aka yi aikin, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aiki. Haka nan kuma akwai bayanau na yanayi, wanda shi kuma nuni yake zuwa ga yadda aka aiwatar da aikin, ko za a aiwatar ko kuma ake aiwatar da aikin.[1]
↑Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.