Movatterモバイル変換


[0]ホーム

URL:


Jump to content
WikipediaInsakulofidiya ta kyauta
Binciko

Bararoji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bararoji
lifestyle(en)Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare natransient and migrant people(en)Fassara
Residence(en)Fassarano value
Has characteristic(en)Fassarano fixed abode(en)Fassara danomadism(en)Fassara
Hannun riga dasedentism(en)Fassara

Bararoji koBororo na nufin rayuwar mutanen da ba su da cikakken wuri guda da suke zama, suna yin hijira daga wuri zuwa wuri domin neman abin da zai taimaka musu wajen rayuwa, kamar ciyar da dabbobinsu ko samun ruwa da sauran albarkatu. Wannan nau’in rayuwa yana da alaƙa da yanayi,noma,kiwo, kokasuwanci, bisa ga buƙatu da yanayin yankin da suke zama.[1][2][3]

Nau’ukan Bararoji

[gyara sashe |gyara masomin]

Akwai nau'ukan rayuwar bararoji kamar haka:

  • Makiyaya: Wannan yana nufin mutane da suke kiwon dabbobi kamar shanu, tumaki, rakuma, da awaki, inda suke tafiya daga wuri zuwa wuri domin samun ciyawa da ruwa ga dabbobinsu. Misali, Fulani makiyaya a Najeriya.[4][5]
  • Tattalin Arziki: Wannan yana nufin 'yan kasuwa fatake da suke tafiya daga wuri zuwa wuri domin ciniki, kamar 'yan kasuwar karni na baya.
  • Manoma: Wasu bararoji manoma, inda suke noma a wuri guda na ɗan lokaci kafin su koma wani wuri.


Amfani da Matsaloli

[gyara sashe |gyara masomin]

Amfani

[gyara sashe |gyara masomin]
  • Ƴan Bararoji suna taimakawa wajen yada al’adu da harsuna.
  • Yana taimaka wajen ci gaba da samar da kayan abinci kamar madara, nama, da fata.
  • Yana ba da dama ga kasuwanci da musayar kayayyaki.[6]


Matsaloli

[gyara sashe |gyara masomin]
  • Sau da yawa suna fuskantar rikici kan filaye tsakanin makiyaya da manoma.
  • Rashin tabbas na muhalli kamar fari ko ambaliya na iya haifar musu da matsaloli.
  • Rashin samun isassun kayan more rayuwa kamar ruwa, asibiti, da makaranta.[6]

Hotunan Gallery

[gyara sashe |gyara masomin]

Manazarta

[gyara sashe |gyara masomin]
  1. https://dictionary.cambridge.org/dictionary/english/nomadic
  2. https://study.com/academy/lesson/nomadic-lifestyle-definition-lesson-quiz.html
  3. https://www.discovermagazine.com/planet-earth/what-is-a-nomad-and-are-there-any-nomadic-tribes-that-still-exist
  4. https://www.peoplegroups.org/Explore/groupdetails.aspx?peid=42667
  5. https://www.jstor.org/stable/715596
  6. 6.06.1https://www.novo-monde.com/en/nomadic-life/
Daga "https://ha.wikipedia.org/w/index.php?title=Bararoji&oldid=577017"
Rukuni:

[8]ページ先頭

©2009-2025 Movatter.jp