| Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| Haihuwa | Jahar Katsina, 19 ga Afirilu, 1997 (28 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
| ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin | |||||||||||||||||||||||||||||||
| Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||
| Lamban wasa | 14 | ||||||||||||||||||||||||||||||
| Nauyi | 68 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||
| Tsayi | 170 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||

Azubuike Godson Okechukwu (An haife shi ranar 19 ga watan Afrilu, 1997). ɗan wasan ƙwallonƙafa ta ƙasar Najeriya da ke buga ƙwallo a ƙungiyar clubstanbul Başakşehir ta kasarTurkiyya a matsayin ɗan wasan tsakiya.
Anhaifeshi aKatsina, Okechukwu ya bugawa ƙungiyoyin Bayelsa United da Yeni Malatyaspor ƙwallon ƙafa.
A ranar 19 ga watan Agusta 2018, Okechukwu ya koma ƙungiyar Pyramids FC ta Premier ta Masar.[1][2]
A watan Janairun 2019, ya koma Çaykur Rizespor a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana. A ranar 10 ga Yulin 2019, İstanbul Başakşehir ya tabbatar, cewa sun sanya hannu kan Okechukwu kan yarjejeniyar aro na tsawon lokaci.[3] Ya lashe gasar ta Turkiyya tare da kulab din.
A watan Agusta na 2020, Okechukwu ya sanya hannu kan kwangilar dindindin tare da İstanbul Başakşehir.
Okechukwu ya fara buga wa ƙasar wasa ne a ƙungiyarkwallon kafa ta kasa a shekarar 2016, kuma Najeriya ce ta zabe shi a cikin jerin 'yan wasa 35 na wucin gadi da za su buga gasar Olympics ta bazara ta 2016.