Wani Gini Mai tarihi a Armaniay a yamacin turaimurnar samun 'yanci a (1920) Armeniya
Armeniya Armeniya, a hukumance jamhuriyar Armeniya, ƙasa ce a yammacin nahiyarAsiya daTurai. Tana iyaka da Turkiyya daga yamma, Georgia daga arewa, da kuma Lachin corridor (karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Rasha), tare da Azarbaijan daga gabas, sai Iran da Azarbaijan da ke yankin Nakhchivan daga kudu. Yerevan shine babban birnin kasar kuma birni mafi yawan jama'a.[1]
Armeniya ƙasa ce da ta ginu a tsarin mulki na bai ɗaya, tana da jam'iyyu da yawa, ana kuma gudanar mulkin demokraɗiyya a cikinta, tana da daɗaɗɗun al'adun gargajiya. An kafa ƙasar Armeniya ta farko Urartu a shekara ta 860, BC, kuma a ƙarni na 6, BC ta maye gurbinta da Satrapy na Armeniya. Masarautar Armeniya ta yi ƙarfi ne a ƙarƙashin Tigranes the Great a karni na 1 BC kuma a shekara ta 301, ta zama kasa ta farko a duniya da ta ɗauki addinin Kiristanci a matsayin addininta na hukuma farkon karni na 5.[2]
Armeniya tana da yanki mai faɗin kilomita 29,743 (sq mi 11,484). Ƙasar galibi tana da tsaunuka, tare da koguna masu guduna, da dazuzzuka kaɗan. Ƙasar ta haura zuwa mita 4,090 (ƙafa 13,419), sama da matakin teku a Mount Aragats, kuma babu wani wuri da yake ƙasa da mita 390, (1,280 ft), sama da matakin teku. Matsakaicin girman yankin ƙasar shine na goma mafi girma a duniya kuma tana da yanki masu tsaunuka akalla kaso 85.9%, fiye da Switzerland ko Nepal. Mount Ararat, wanda a tarihi ya kasance a cikin yankin kasar Armeniya, shine tsauni mafi tsayi a yankin mai tsayin mita 5,137, (ƙafa 16,854). A yanzu kuwa yana cikin yankin ƙasar Turkiyya ne, amma kuma bayyane yake a na ganinsa sosai daga Armeniya, Armeniyawa suna ɗaukarsa a matsayin alamar ƙasarsu dalilin kenan da yasa suka saka hoton tsaunin a cikin alamar ƙasar Armeniya har zuwa yau.
Armeniya jamhuriya ce ta demokraɗiyya mai majalisa. Kundin tsarin mulkin Armeniya ya zamo tsarin tafi da mulkin shugabancin jamhuriyar kan gaba har zuwa watan Afrilun 2018.
Bisa kundin tsarin mulkin Armeniya na yanzu, shugaban kasa shi ne wanda ke rike da manyan ayyuka na wakilci, yayin da firaministan kuma shi ne shugaban gwamnati kuma yake gudanar da harkokin zartaswa.Ƙarfin doka yana hannun Azgayin Zhoghov ko Majalisar Dokoki ta ƙasa, wadda ita ce majalisa marar rinjaye.
↑"Human Development Report"(PDF). United Nations Development Programme (UNDP). 2019.Archived(PDF) from the original on 16 July 2020. Retrieved27 July 2020.