babban coci a garin abujaAbuja-college.jpgAbuja millennium parkKofar AbujaAbuja BaBan Birnin taraiyqjami an abujaRCCG birnin abujaCikin Birnin Abuja]Abuja[1] Itace babban birnin tarayya, kuma na takwas a girma aNajeriya[2]. Birnin na nan a tsakiyar ƙasarNajeriya, a cikin Birnin Tarayya (FCT), kuma tsararran birni ne da aka zana a tsakanin shekarun 1980s, wanda mai zane Architect KenzoTange ya zana ta.[3] Ta zama babbar birnin [h[Najeriya
Bayan tsohuwar babban birninLegas[4] a ranar (12) ga watan disambar (December) shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari-tara da cassa in da ɗaya (1991).[5]
Birnin ya koma na tarayya ne tun a lokacin mulkinGen.Ibrahim Babangida[6] a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da cassa in da ɗaya (1991)[7] wanda kafin lokacin birnin tarayyar ya kasance a birninLegas[8] dake kudu maso yammacin Najeriya. Birnin Abuja ya kasance birni ne gagara-misali saboda birnin ya ƙunshi abubuwa da dama wanda ido ne kaɗai zai iya tabbatar da hakan. Inda yake ɗauke da manyan ma'aikatu, makarantu[9], filayen jiragen sama, da filin wasa babba, da dai sauran manya-manyan ma'aikatun gwamnati wanda suke juya akalar ƙasar baki ɗaya. A cikin birnin Abuja akwai mutane a kalla776,298 a kiɗayar da akayi a shekarar (2006), kasan cewar birnin na tarayya[10] ne wato ya tara duk jinsinmutane[11] daƙabilun[12] dake Najeriya gabaki ɗaya, ko wacce jaha a Najeriya tana da wakilai a sassa daban-daban a cikin Abuja domin ganin sun wakilci jihar su a fage da dama don cigaban jihar su. A cikin birnin Abuja akwai wuraren shaƙatawa da dama da wuraren buɗe ido musamman ga baƙi, waɗanda suke muradin kashe kwarkwatar ido ta fagen kallon abubuwan ban al'ajabi, da ɗebe kewa.
Babban al'amari game da labarin ƙasa na Abuja (wato geography) sun haɗa daAso Rock[13], gidan shugaban ƙasa (presidential complex), Majalisar dokoki (National assembly),[14] Kotun ƙoli (supreme court), Sannan yawancin birnin ya mike har zuwa kudancin dutsen, Sannan kumaZuma Rock[15] wanda ke arewacin birnin a bisa babban titin Kaduna.[16]
Manyan wuraren bautan sun haɗa da babbanmasallaci[17] da babban chochi na birnin Abuja, wato Nigerian National Central Mosque da Nigerian National Christian Centre. Birnin na hada-hada dagafilin jirgin saman Abuja watoNnamdi Azikiwe International Airport. Abuja tana ɗaya daga cikin manyan birane da aka tsara kuma ɗaya daga cikin mafi arziƙi.[18]
Abuja itace cibiyar gudanarwa da siyasa na Najeriya. Har wayau tana ɗaya daga cikin manyan birane na (Afurka) musamman matsayin Najeriya a harkokin siyasa da ci gaba.[19] Abuja tana da mahimmanci a harkokin ganawa watau meeting kamar (2003), Commonwealth Heads of Government meeting da kuma (2014)World Economic Forum (Africa) meetings.[20][21]
Garin Abuja a farkon ƙarni na (20), sunan wani gari ne yanzu da ake kiraSuleja.[22] Asalin mazauna AbujaGwari ne, wato mutanenGbagyi, wanda Gbagyi ne yaren farko na garin sai kuma sauran yarika kaman Bassa, Gwandara, Gade,Dibo,Nupe da kumaKoro.[23] An samar da babban birnin a dalilin rabe-raben harsuna a Najeriya.[24] Sauran dalilan kuma sun haɗa da yawan mutanen Legas, wanda ke jawo cunkoso a garin. Sannan bugu da ƙari garin Legas na samun haɓakar kasuwanci cikin sauri, wannan dalilai suka jawo aka maido da babban birnin zuwa Abuja.[25] Wannan tsari da aka bi iri ɗaya ne da yadda Brazil suka tsara babban birninsuBrasilia.
Gwamnatin Soji ta Najeriya a ranar 4, ga watan Febrerun shekara ta 1976, ta fidda tsarin doka mai lamba 6, acikin kundin tsarin mulki wacce ta cire Legas a matsayin babban birnin kasan zuwa Abuja.[26][27] Gwamnatin Soji naMurtala Muhammed da kumaOlusegun Obasanjo ne suka fidda asalin aikin tsarin samar da babban birnin Abuja wanda gamnatin farar hula taShehu Shagari ta karasa.[28]Tsarin gine-gine ya fara acikin shekarun (1970s) amma a dalilin matsalar kudade na siyasa, an karasa aikin a shekarun (1980s) Maido babban birnin Najeriya zuwa Abuja ya jawo rikici sosai kuma babban dan-adawan wannan canji shineObafemi Awolowo.[29] Obafemi Awolowo ya kasance dan siyasan Najeriya mai kuma wakiltan yarbawa acikin kin yarda da maido babban cibiyar kasan daga Legas zuwa Abuja. A lokacin da ake yakin neman zabensa na shugaban kasa, ya sha alwashin cewa idan ya zamo shugaba zai gayyato kamfanin "Walt Disney Corporation" don su mayar da Abuja wajen shakatawa.[30] Amma kash, samun nasarar shugaban ƙasan farar hula na farko wato shehu shagari ya sa an fara ci gaba da habaka gine-gine a babban birnin inda ya nemi 'yan kwangila da 'yan kwadago da su dage wajen kammala aikin a cikin sauri. Bayan dawowarsa ya nuna rashin gamsuwar sa akan yadda aikin ya dau tsawon lokaci gaAlhaji Abubakar Koko.[31]
An baiwa kamfanin International Planning Associates (IPA) kwangilar kawo tsarin zanen Abuja a shekarar (1977). wanda sashin gwamnatin tarayya watau Federal Capital Development Authority (FCDA) suka bada kwangilan.[32]A yanda nasaban tsarin yarjejeniyar ta nuna, tsarin ya ƙunshi al'ammomi daban daban, wanda suka hada da zaban wajen da zai zama gidan gwamnati, tsarin yadda yankuna da birane zasu kasance da kuma kundi na tsare-tsare da na cigaba.[33]
Abuja Municipal Area Council ke gudanar da harkokin birnin Abuja. Bugu da ƙari akan harkokin ayyukan gwamnati birnin shine cibiyar gwamnatin tarayyar Najeriya kuma har wayau tushen siyasa da gudanarwa na gwamnatin ƙasar.
Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ce ke tafiyar da babban birnin tarayya, wanda ministan da shugaban kasa ya zaba na (FCT) ke shugabanta. Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ce ke kula da ayyukan gine-ginen da abubuwan more rayuwa na yankin. A yanzu haka tsohon gwamnan RiversNyesome Wike shine ministan babban birnin tarayya.[34]
Abuja a tsarin rabe-raben Koppen ta faɗa a ajintropical wet and dry climate (Köppen:Aw). Garin na fuskantar yanayi iri uku, sanyi, zafi da kuma lokacin ɗumi da ruwan sama. A tsakanin waɗan nan yanayi akwai lokacin sanyi da hazo.
Ruwan sama a Abuja yana farawa ne daga watan Aprilu sannan ya ƙare a watan October, a yayin da zafin hasken rana yake kaiwa makin 28 °C (82.4 °F) zuwa 30 °C (86.0 °F) sannan kuma sanyin dare a maki mafi ƙarancin yana kaiwa 22 °C (71.6 °F) zuwa 23 °C (73.4 °F). Amma a lokacin rani, zafin haskenrana a bisa maki mafi girma yana kaiwa 40 °C (104.0 °F) amma yanayin yana sauƙi da dare akan makin ma'aunin celcius 12 °C (53.6 °F). har zuwa ƙarshen dare yana kaiwa 30 °C (86.0 °F). wannan shine adadin makin sauyin yanayi da sashin birnin Abuja ke fuskanta a taƙaice.
[[File:Secret garden in Riverplate park - Abuja.jpg|Secret garden in Riverplate park - Abuja
Wannan ita ce kofar shiga birnin tarayya AbujaWannan shine babban Masallacin AbujaWannan shine babban Majami'ar Abuja kenanAbujaBabban filin tashi da saukar jiragen sama na abujaNicon luxury hotal abujaSitadiyo ta kallo a AbujaOfishin Majalisar Wakilai Wannan dutsen zuma kenan a yankin AbujaGinin majalissar wakilai ta abuja
↑Murray, Senan. "Life of poverty in Abuja's wealth."BBC. Tuesday 13 February 2007. Retrieved 12 September 2011.
↑The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City (2020)". Retrieved 23 January 2021.
↑The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City 2020". Retrieved 12 May 2020.
↑Aso Rock Declaration on Development and Democracy: Partnership for Peace and Prosperity | The Commonwealth".thecommonwealth.org. Retrieved 30 May 2020.
↑The New Federal Capital". fcda.gov.ng. (2018). Archived from the original on (19) May (2020). Retrieved (5) January (2021).
↑Abuja | Geography, Development, & Population | Britannica".www.britannica.com. Retrieved 5 January 2022.
↑"Yusuf, Omotayo (1 October 2015). "#NigeriaAt55: Top 5 Reasons Nigeria's Capital Was Moved From Lagos To Abuja (PHOTOS.
↑Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 167–175. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 5 January 2022.
↑Yusuf, Omotayo (1 October 2015). "Why The Capital Was Moved From Lagos To Abuja".Naija.ng – Nigeria news.
↑Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 167–175. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 5 January 2022.
↑Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 173. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 22 September 2020.
↑Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital".The Journal of Modern African Studies.22 (1): 173.doi:10.1017/S0022278X00056846.JSTOR 160334. Retrieved 22 September 2020.
↑Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital".The Journal of Modern African Studies.22 (1): 174.doi:10.1017/S0022278X00056846.JSTOR 160334. Retrieved (22) September 2020
↑Elleh, Nnamdi (2001).Abuja, the single most ambitious urban design project of the 20th century.ISBN9783897391659.
↑Shuaibu, Umar. "Unsung heroes of Abuja master plan". Retrieved 22 September 2020.